1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya tana kara karfi a Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar SB)(MAB
October 28, 2022

Sayar da makamai da suka hada da jirage masu sarrafa kansu na kara karfin Turkiyya a nahiyar Afirka. Inda Turkiyya ke sayar da karin makamai ga nahiyar.

Turkiyya I Erdogan I Makamai
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na TurkiyyaHoto: Kayhan Ozer/AFP

Turkiya na karafafa dangantakarta ta tsaro da nahiyar Afirka, bayan kwashe sama da shekaru 10 tana karfafa tasirinta a huldar tattalin arziki da al'adu a nahiyar. A kwanakin baya-bayan nan, Turkiyya na yin cinikin makamai tsakaninta da kasashen Afirka musamman ma yankin yammacin Afirkan. Tuni ma ta sanya hannu kan yarjejeniyar huldar sojo tsakaninta da kkasashe masu yawa a Afirka.

A shekara ta 2021 yawan jiragen yakin da Turkiyya ke sayarwa Afirka ya ninka sau 10, inda cinikin makaman da ta yi ya tashi daga dalar Amirka miliyan 82 da dubu 900 a 2020 zuwa dalar Amirka miliyan 460 da dubu 600.

Duk da cewa har kawo yanzu kasa da kaso biyar na makamai ne kacal Afirka ke saya daga Turkiyyan, cinikin makaman tsakaninta da Afirkan na habaka cikin sauri kamar yadda wani bincike da Cibiyar Nazarin Harkokin Tsaro ta Kasa da Kasa ta Jamus ta yi dangane da tasirin Turkiyyan a Afirka ya nunar.

Taron Afirka da TurkiyyaHoto: Emrah Yorulmaz/AA/picture alliance

Yayin da ake fama da hare-haren masu ikirarin jihadi a yankin gabashi da yammacin Afirkan ba ya ga rikicin cikin gida, kaksashen nahiyar na kara karfafa matakan tsaro. A wata hira da ya yi a shekarar da ta gabata ta 2021, shugaban kasar Turkiyyan Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa kasashen Afirka sun bukaci tallafinsu kan jirage marasa matuka.

Ovigwe Eguegu mai sharhi kan al'amuran siyasa a Najeriya, akwai bukatar tallafi kan tsaro tsakanin bangarorin sannan ya kara da cewa a yanzu da Afirka za ta cimma yarjejeniyar cinikin makamai da kasashen Rasha da Chaina,  Amirka za ta fitar da sanarwa cewa Rasha na kara karfi a Afirka kuma tana barazana ga muradunta. Amma kasancewar Turkiyya mamba a kungiyar tsaro ta NATO, ya sanya ta samu dama fiye da Rasha da Chaina. 

Turkiyya ta sanya hannu kan yarjejeniya da ke da nasaba da aikin soja da kasashen yammaci da gabashin Afirka. Wannan dai ka iya hadawa da ziyarar sanin makamar aiki da cibiyoyin bincike da musayar ma'aikata a tsakanin cibiyoyi da kamfanoni. Sojojin Najeriya sun gudanar da atisaye na amfani da jirage marasa matuka a Turkiyya, yayin da tun daga shekara ta 2020 Ankran ke bai wa jami'an 'yan sandan kasar Kenya horo.