Erdogan na son dorewar yarjejeniyar Idlib
February 14, 2019Talla
A cewar Erdogan Turkiyya ba ta muradin karin ganin wani tashin hankali da al'umma ke shiga a yankin na Idlib da ke kusa da iyakar Turkiyya ko wani bangare na kasar ta Siriya. Erdogan ya bayyana haka ne a lokacin taron manema labarai da aka nuna ta kafar talabijin lokacin taron koli da ya halarta tare da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin da Hassan Rouhani na Iran a birnin Sochi da ke a kudancin Rasha.
Erdogan ya ce dukkanin shugabannin sun amince ba sa muradin ganin duk wani tashin hankali na sojoji bayan da Turkiyya ta kara daukar wasu matakai na musamman don ganin zaman lafiya ya samu a yankin. Ya ce sun kuma amince cewa shirin fitar dakarun Amirka daga Siriyar abu ne me kyau.