1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokoki na nazarin tura dakarun kasar Libiya

Abdoulaye Mamane Amadou
January 2, 2020

Majalisar dokokin kasar Turkiyya na shirin bayyana matsayinta game da yunkurin shugaban kasar na tura dakarun sojan Turkiyya zuwa kasar Libiya.

Türkei l Erdogan will Truppen nach Libyen schicken - Militär
Hoto: Getty Images/B. Kara

Nan gaba a yau din nan ne ake sa ran majalisar zata tafka mahawara a kan batun, kana kuma masu sharhi na cewa jam'iyyar AKP ta shugaba Recep Tayyip Erdogan da kawancenta ta MHP  na da adadin 'yan majkalisun da ke iya basu gagarumin rinjayen domin yin n'am da kudrin dokar.

A karshen watan Nuwamban da ya gabata na shekarar bara ne dai shugaba  Erdogan, ya cimma wata yarjejeniyar tsaro da gwamnatin kasar Libiya mai goyon bayan MDD karkashin jagorancin Fayez al-Sarraj a wani yunkuri na tallafa mata yakar dakarun sojan da ke biyayya ga Khalifa Haftar mai yunkurin kwace mulki daga gwamnatin kasar.