1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta ƙuduri ƙaƙaba takunkumi akan Siriya

October 5, 2011

Firaministan Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce ƙasarsa za ta ƙaƙaba takunkumi akan Siriya duk kuwa da karan tsaye da aka yi ga matakin komitin sulhu na yin hakan

Bashar al-Assad da Recep Tayib ErdoganHoto: AP

Ƙasar Turkiyya ta ce za ta ƙaƙaba takunkumi na gaban kanta akan tsohuwar aminiyarta Siriya, duk kuwa da matakin da aka dauka na hana wa Majalisar Ɗinkin Duniya(MƊD) ƙaƙaba takunkumi akan shugaba Bashar Assad bisa matakin da yake ɗauka akan masu zanga zangar nuna adawa da gwamnatinsa. Fraiministan Turkiyya, Reccep Tayyip Erdogan ya bayyana ɓacin ransa game da matakin wuce gona da iri rashin sanin da Assad ke dauka. Mutane sama da 2,700 ne dai suka rasa rayukansu a cikin zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Assad da aka fara a watan Maris. A jiya 04.10.2011 ne dai ƙasashen Rasha da China suka hau kujerar na-ƙ akan ƙudurin komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Allah wadai da matakin da ake ɗauka domin murƙushe 'yan zanga-zangar nuna adawa da gwamnati a Siriya. Ƙasar Faransa ce ta zayyana wannan ƙudurin da taimakon sauran ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai da suka haɗa da Jamus.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi