Turkiyya ta amince da tsagaita wuta a Siriya
October 17, 2019![Militärischer Konflikt in Nordsyrien | Türkischer Präsident Recep Tayyip Erdogan mit US-Vizepräsident Mike Pence](https://static.dw.com/image/50874034_800.webp)
Talla
A wani sakon a shafinsa na Twitter, Shugaba Trump ya ce wannan labari na ceton rayukan miliyoyin mutane a yankin Kurdawa, abin farin ciki ne matuka.
A wata ganawar da ta wakana tsakanin mataimakin shugaban Amirka Mike Pence da shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan, Amirka da Turkiyya sun amince kan tsagaita buda wuta a arewacin Siriya.
Mr. Pence ya tabbatar da hakan ne 'yan mintuna bayan ganawar da suka yi a Ankara babban birnin kasar Turkiyya.
A wannan Alhamis ne dai mataimakin shugaban na da ministan harkokin wajen kasar Mike Pompeo suka isa Turkiyya a kokarin kawo karshen hare-hare kan kan Kurdawan na Siriya.