Turkiyya da Isra'ila sun sake dawo da huldar a tsakaninsu
March 9, 2022Talla
Tuni dai ma fadar gwamnatin Ankara da ta jima tana 'yar tsama da Isra'ila, ta bayyana muhimmancin da ke da akwai na ci gaba da tattaunawa, ko baya ga kara tabbatar da huldar kasahen biyu kan batutuwan da dama da suka shafi tsaro da tattalin arziki.
Shugaba Isaac Herzog na Isra'ila, na a matsayin shugaban farko da ya kai ziyara a kasar Turkiyya, tun bayan shekarar 2007 da rikici ya barke a tsakanin kasashen biyu game da batun goyon bayan kasar Falasdinu.
Ziyarar wacce aka shafe tsawon makwanni ana shiryata na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen biyu na Turkiyya da Isra'ila, suka bayyana anniyarsu ta sulhunta rikicin da ya barke tsakanin Rasha da Ukraine a baya bayan nan.