1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta kai tallafi Somaliya

August 19, 2011

Tawagar Firaministan Turkiyya ta fara rangadin wuraren da suka fi fama da matsalar fari a Somaliya domin bayar da tallafi

Recep Tayyip Erdogan - Frime Ministan TurkiyyaHoto: dpa

Firaministan ƙasar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya ziyarci yankunan da suka fi fama da matsalar fari a Mogadishu, babban birnin ƙasar Somaliya, a wani abinda ke zama ziyara ta farko da wani fitaccen shugaba yayi cikin kusan shekaru 20 da ƙasar ta Somaliya ta yi tana fama da rigingimu. Ƙasar ta Somliya ce, ke kan gaba wajen fuskantar matsalar farin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewar ya ɓarke a ƙasashen yankin gabashin Afirka- ciki kuwa harda birnin Mogadishu. Erdogan, wanda ministocin gwamnatin sa huɗu da matarsa ke rufawa baya, sun ziyarci wani sansanin 'yan gudun hijira da kuma wani asibitin dake birnin na Mogadishu, inda kimanin mutane dubu 100 da suka tserewa matsalar farin ke samun kulawa. Ziyarar ta Firaministan na Turkiyya ta zo ne bayan wani taron da ƙungiyar ƙasashen Musulmai ta O-I-C ta yi, a birnin Istanbul na ƙasar ta Turkiyya, inda mambobin ƙungiyar suka yi alƙawarin samar da tallafin daya kai dala miliyan 350 ga 'yan Somaliyar da matsalar farin ta ɗaiɗaita.

Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Umaru Aliyu