1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta mayar da martani ga Merkel

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 22, 2018

Mahukuntan kasar Turkiyya sun bayyana kalaman suka da Merekel tai wa Turkiyyan dangane da matakin soja da take dauka a yankin Afrin na Siriya da abin takaici.

Bundestag - Angela Merkel gibt Regierungserklärung ab
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa/C. Gateau

A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Turkiyya ta fitar, ta bayyana kalaman na Merkel da cewa ta yi su ne ba tare da tana da cikakken bayani kan abin da ke afkuwa a Afrin din ba, tana mai cewa abin takaici ne wasu kawayen Turkiyya na kallon lamarin da kuma daukar bayanai daga bangaren 'yan ta'adda, abin da Ankaran ta ce ba za su aminta da shi ba. A karon farko ne dai Merkel din ta bayyana cewa abin takaici ne ace ana kashe fararen hular yankin Afrin na Siriyan, tare da tilasta musu barin gidajensu sakamakon matakan sojan da Turkiyya ke dauka a yankin.