Ruruwar rikicin diflomasiyya tsakanin Amirka da Turkiyya
August 15, 2018Shugaban na Turkiyya ya yi kira a kauracewa kayayyakin latroni na kasar Amirka irinsu wayar hannu na kamfanin Aple. A cikin wannan rikici na diflomasiyya tsakanin Turkiyya da Amirka, a wannan Laraba ce kuma mai martaba sarkin Katar Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani ya kai wata ziyara birnin Ankara na kasar ta Turkiyya a wani mataki na nuna goyon bayansa ga Shugaba Recep Tayyip Erdogan, da kasarsa ke fuskantar matsalar tattalin arziki da kuma rikicin diflomasiyya da Amirka.
Yayin wata ganawa da ya yi da shugaban na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, sarkin Katar Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani, ya yi wa kasar Turkiyya alkawarin zuba jarin da zai kai na Dala miliyan 15 kuma ba da jimawa ba, kamar yadda fadar shugaban kasar ta Turkiyya ta sanar.
Daga cikin kayayyakin da Turkiyya ta saka wa karin haraji, akwai motocin yawon buda ido da kashi 120 cikin 100, da kayayyakin barasa na Amirka da kashi 140 cikin 100, sai taba sigari ta Amirka da kashi 60 cikin 100 da su shinkafa da sauran kayayyakin shafe-shafe na Amirka.