EU ta daina kasuwanci da kamfanin Turkiyya
September 22, 2020Talla
Ministocin kungiyar Tarayyar Turai sun amince da katse huldar kasuwanci da kamfanonin uku na kasashen Turkiyya da Kazakhstan da Jordan da aka samu da safarar makamai tun watan Junin 2020.
Sai dai ana ganin sanya wa kamfanin Turkiyya takunkumi zai iya tada kwantaccen rikici tsakanin Ankara da kasashen EU a kan arzikin mai da makamashin iskar Gas da ake takaddama a gabashin Tekun Bahar Rum.