1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Erdogan: Mun shirya kai hari Siriya

Abdul-raheem Hassan
October 8, 2019

A wani mataki na tauna aya domin tsakuwa ta ji tsoro, Shugaba Raccep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya ce ya kammala shirin tura dakarun yaki kan iyakar kasarsa da Siriya da nufin kaddamar da hare-hare kan mayakan Kurdawa.

Türkischer Kampfhubschrauber T129
Hoto: picture-alliance/AA/C. Oksuz

Da ya ke tsokaci kan wanna mataki, Shugaba Erdogan ya ce "Lokaci ya yi da zamu share hanyar wanzuwar zaman lafiya. Za mu iya kai farmaki a kowane lokaci. Za mu kaddamar da harin ta sama da ta kasa. Muna da yakinin samun goyon bayan kawayenmu da ke Siriya." 

Sama da wata guda kenan Shugaba Erdogang ke barazanar kai samamen soja kan mayakan Kurdawa a arewacin Siriya. Matakin na Turkiyya na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Amirka ke janyewa daga bakin daga a Arewa maso Gabashin kasar Siriya. Matakin da ke shan suka daga kawayen Siriya da sauran kasashen duniya.