Turkiyya za ta hada manya don ceto Siriya
July 29, 2018Talla
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya ya ce zai karbi bakuncin wani taron koli da zai dubi halin da kasar Siriya da yaki ya daidaita ke ciki.
A jawabin da ya yi wa 'yan jaridu a wannan Lahadin, Shugaba Erdogan ya ce taron da zai hada da kasashen Rasha da Faransa da kuma Jamus, za a yi shi ne a Istanbul babban birnin Turkiyya.
A makon da ya gabata, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ministanta na harkokin waje Heiko Maas, sun gana da Sergei Lavrov na Rasha da wani babban sojin Rasha, inda suka tattauna halin da Siriya ke ciki.
Ana dai sa ran kasashen za su tattauna batun komawar Siriyawan da ke hijira a ketare ne.