1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Turmutsitsi ya yi sanadiyyar rayukan mutun 11 a Indiya

Zainab Mohammed Abubakar
June 4, 2025

Mutanen sun mutu ne a yayin da suke bukin murnar nasarar da kungiyar wasan kurket ta samu a birnin Bengaluru.

Hoto: Biswakalyan Purkayastha/DW

Magoya bayan 'yan wasan kurket cikin farin ciki sun yi dafifi don taryar jaruman su, da ake kira Royal Challengers Bengaluru, bayan sun doke Punjab Kings a wasan karshe na gasar kurket na Premier ta Indiya a daren Talata.

Amma farin cikin na dimbin jama'a ya rikide zuwa bakin ciki da jimami, wanda da Firaminista Narendra Modi ya kira shi da babban tashin hankali. Babban ministan jihar Karnataka Siddaramaiah ya ce, mutane 11 da suka mutu matasa ne, daura da wasu 47 da suka jikkata.

Ya kara da cewa, babu wanda ya yi tsammanin fitowar jama’a irin wannan, kasancewar filin wasan yana da karfin daukar mutane dubu 35 kacal, amma wajen mutane dubu 200 zuwa 300 ne suka zo.