1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iKenya

Turmutsutsi wajen karrama gawar Odinga

Abdullahi Tanko Bala
October 17, 2025

Kenya na gudanar da zaman karrama gawar jagoran adawa Raila Odinga wanda shugaba William Ruto ya jinjina wa a matsayin jigon dimukuradiyya a kasar.

Masu zaman makokin mutuwar Raila Odinga a filin wasa na Nyayo a Nairobi
Masu zaman makokin mutuwar Raila Odinga a filin wasa na Nyayo a NairobiHoto: Thomas Mukoya/REUTERS

Gomman mutane sun jikkata yayin wani turmutsutsi wajen zaman makoki na karramawa da aka yi wa gawar madugun adawa Raila Odinga a Nairobi babban birnin kasar Kenya.

Gidan talabijin din Kenya NTV ya wallafa wani hoto a shafin X jami'an agaji na bayar da kulawa ga wasu masu zaman makoki da suka sami raunuka.

Majiyoyi daga asibitoci sun ce an kwantar da akalla mutane 17 bayan turmutsutsin

Wannan na faruwa ne kwana guda bayan da jami'an tsaro suka bude wuta kan mai uwa da wabi domin tarwatsa dandazon masu makoki inda suka kashe akalla mutane uku.