1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Toshe 'yan jarida ya ja wa Twitter suka

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 16, 2022

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta kan abin da ta kira da karfa-karfa na kamfanin Twitter, sakamakon matakin da ya dauka na toshe shafukan wasu 'yan jarida.

Elon Musk | Twitter | Suka
Kamfanin Twitter da shugabansa Elon Musk na shan sukaHoto: Dado Ruvic/REUTERS

Kakakin Majalisar Dinkin Duniyar Stephane Dujarric ne ya bayyana damuwar, inda ya kara da cewa bai kamata a rinka toshe bakin 'yan jarida a shafukan da ke ikirarin kare 'yancin fadar albarkacin baki ba. A cewarsa matakin na kamfanin Twitter na da munin gaske, ganin ya zo ne a daidai lokacin da 'yan jarida a duniya baki daya ke fuskantar matsin lamba da cin zarafi da barazana.