Hukunta wasu mutane masu hannu a shan gubar Alexeï Navalny
October 14, 2020Talla
Wata majiya daga hukumar EU tace an aike wa kasashe membobin kungiyar bukatar daukar muhimman takunkuman a rubuce domin su tabbatar da amincewarsu, kafin wallafa sunayen wadanda lamarin ya shafa da kuma soma aiki da matakin a gobe Alhamis.
Tun daga farko dai ministocin harkokin wajen kasashen da suka gana a ranar Litinin din da tagabata sun yi na'am da gagarumin rinjaye kan shawarwarin takunkuman da kasashen Jamus da Faransa suka gabatar, kana kuma babban jami'in diflomasiyar Turai Josep Borrell ya bayyana cewa daukacin kasashen sun aminta da matakan.