Ukraine da kawayenta na taro a Paris kan tsaronta bayan yaki
January 6, 2026
Bisa shirin Donald Trump na shiga tsakani don kawo karshen yaki da Rasha ne kasashen Turai da ke dasawa da Ukraine ke taro da wakilan Amurka a birnin Paris domin tattauna batun tabbatar da tsaro a Ukraine.
Wakilan kasashe 35 ciki har da shugabannin kasashe 27 na neman daidaita matsaya tsakanin Washington, Kyiv da Turai kan kyautatuwar tsaro a Ukraine, don kawo karshen rikicin mafi muni da aka fuskanta a nahiyar Turai tun bayan kawo karshen yakin duniya na biyu.
Karin bayani: Shawari 28 na sasanta Ukraine da Rasha
Wakilin musamman na shugaban Amurka Donald Trump, Steve Witkoff da surukinsa Jared Kushner, za su halarci taron kawancen, wanda Faransa da Burtaniya suka kaddamar a bazara.
Shugabannin na neman hanyar fuskantar alkibla guda kan hanyoyin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Ukraine da Rasha, da kuma matakan da za a dauka a kan kasar da za ta saba w alkawari. Kazalika za su tattauna batun tura rundunar sojoji ta kasa da kasa don kare Ukraine,a matsayin wani bangare na yarjejeniyar, a cewar fadar shugabankasar Faransa.