1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wutar lantarki ta katse a kasashen Ukraine da Moldova

January 31, 2026

Ukraine da makwafciyarta Moldova sun fuskanci matsalar daukewar wutar lantarki. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Ukraine ke fama da matsala da manyan layukan wutarta.

An samu tsaiko a tashoshin jiragen kasa na Kyiv sakamakon katsewar wutar lantarki
'Yan Ukraine da ke tsaye a tashar jirgin kasa cikin sanyiHoto: Alina Smutko/REUTERS

Matsalar katsewar wutar lantarki a birnin Kyiv ta haifar da daukewar ruwan sha da kuma tsaiko a tashoshin jiragen kasa. Ministan makamashi na Ukraine, Denys Shmygal ya tabbatar da aukuwar lamarin da ya bayyana a matsayin tangardar na'urori.

Karin bayani:Rasha ta sake kai hari kan tashoshin makashi a Ukraine 

Su ma wasu yankunan Moldova sun kasance cikin dubu, yayin da wutar da ke ba da hannu a kan hanyoyi sun tsaya cik. Cibyoyin makamashin Ukraine sun sha fuskantar hare-hare tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a kasar. A ranar Juma'ar ce fadar Kremli ta ce Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya amince da tsagaita kai farmaki birnin Kyiv na tsawon mako guda, bisa bukatar takwaransa na Amurka, Donald Trump.