1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

FIFA za ta dakatar da Rasha daga wasanni

February 28, 2022

Birtaniya ta ce za ta hana 'yan kasuwar Rasha sama da miliyan uku yin wata hada-hadar kudi da kamfanonin Birtaniya. A jimlance kasashen Turai 19 ne suka mayar wa Rasha martani ga mamayar da  ta yi wa Ukraine.

Zurich FIFA Praesident Gianni Infantino beim digitalen FIFA-Kongress
Hoto: ULMER Pressebildagentur/imago images

Hukumar kula da kwalllon ta duniya, FIFA, ta ce za ta dakatar da Rasha daga cikin gasar da take shiryawa. Matakin na FIFA ya biyo bayan shawarar da kwamiti mai kula da wasannin Olympic na duniya ya bayar cewa bai kamata a bar 'yan wasan Rasha da Belarus su ci gaba da bugawa wasanni na kasa da kasa ba, a wani mataki na mayar da martani ga mamayar da Rashan ta yi wa Ukraine.

Sai dai Shugaba Putin na Rasha ya mayar wa Faransa da sauran kasashen yamma martanin cewa  kwace ikon da Rasha ta yi da yankin Crimea a baya shi ne abin da zai kawo karshen tashin hankali.