1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai hari kan wani sansanin soji

Abdoulaye Mamane Amadou
March 13, 2022

A yayin da rikicin Rasha da Ukraine ke shiga mako na uku, dakarun tsaron Rasha sun yi ruwan wuta kan sansanin sojan Ukraine da ke lardin Lviv kusa da iyakar kasar da Poland.

Ukraine - Konvoi prorussischer Truppen außerhalb von Volnovakha
Hoto: Alexander Ermochenko/REUTERS

Wata majiya daga yankin ta shaida wa manema labarai cewa Rasha ta kaddamar da harin rokoki ne kan wata cibiyar horar da jami'an tsaro, to amma sai dai kawo yanzu ba a kammala tattara muhimman bayanai don gano adadin wadanda suka jikkata ba a wata sanarwa da kantoman yankin ya fitar.

Rikicin kasashen dai ya shiga mako na uku, kana kuma har yanzu duk da kiraye-kirayen tsagaita wuta da matsin lamba daga manyan kasashen yamma, Rasha na ci gaba da tsanta hare-hare ko ta ina a Ukraine a yunkurinta na mamaye kasar.

Fiye da mutun miliyan biyu da rabi ne suka yi hijira daga Ukraine don samun mafaka a wasu kasashen da ke makwaftaka da kasar ciki har Poland wacce ta karbi akalla miliyan daya da rabi.