Ko mai Ukraine za ta bai wa Afirka?
January 4, 2023Masu nazarin lamuran kasa da kasa na da ra'ayin cewar dangantaka ta kut da kut tsakanin kasashen Afirka da Ukraine, za ta bayar da damarmaki ga dukkan bangarorin. Wannan na zuwa ne bayan da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya sanar da cewa, za a bude sababbin ofisoshin jakadancin Kiev a nahiyar Afirka a watanni uku na farkon shekarar nan ta 2023. A wani jawabi da ya yi a farkon watan Disamban shekarar da ta gabata, Zelensky ya sanar da cewar Ukraine na shirin kaddamar da dangantaka da gomman kasashen Afirka.
Karin Bayani: Rasha na son tura wa Mali da takin zamani
Tuni aka gano kasashe 10, wadanda za a bude sababbin ofisoshin jakadancin Ukraine din a Afirka. A cikin watan Oktobar bara ministan harkokin wajen kasar Dmytro Kuleba ya kai rangadi a wasu kasashen Afirka, a wani yunkuri na karfafa huldar diflomasiyya. Tafiyar da ya katse ala tilas, bayan da Rasha ta kai jerin hare-haren makamai masu linzami kan garuruwan Ukraine a lokaci guda. Tun farkon mamayar Rasha ne Ukraine ta yi ta kokarin samun goyon baya a nahiyar Afirka, yayin da tasirin da Rasha ke da shi a nahiyar ke ci gaba da samun tagomashi.
Ko da yake Zelensky bai ambaci sunayen kasashen da za a bude wadannan ofisoshin jakadanci ba, wakilin Ukraine na musamman a yankin Gabas ta Tsakiya da Afirka Maksym Subkh ya shaidawa kafar yada labaran Ukraine cewa za a fara mai da hankali kan kasashen Afirka da ke yankin Kudu da Sahara. Oleh Belokolos tsohon jami'in diflomasiyyar Ukraine kuma manazarci na kasashen waje ya fadawa tashar DW daga birnin Kieve cewar, lokaci ya yi da Ukraine za ta bayyana a kasashen Afirka. A cewar sanarwar shugaba Zelensky dai ba wai Ukraine na da ra'ayin bude ofisoshin jakadanci saboda dalilai na samun wakilci a matakin diflomasiyya a Afirka kadai ba ne, amma za ta kuma yi la'akari da wasu muhimman batutuwa kamar bangaren kasuwanci.
Karin Bayani: Ukraine na samun nasara kan sojojin Rasha
Dokta Boni Yao Gebe wani manazarci kan Afirka kuma babban jami'in bincike a cibiyar kula da harkokin kasa da kasa da diflomasiyya ta jami'ar Ghana, ya yi imanin cewa watakila kasashen Afirka za su canza salon yadda suke shiga fannin hadin gwiwa da kasashen yammacin Turai. Maimakon yin shawarwari a daidaikunsu kamata ya yi kasashen Afirka su shiga wannan yarjejeniya a kungiyance, domin karin yawan ribar da za su samu. Abin tambayar dai shi ne, mai yasa Kiev ke zawarcin kasashen Afirka a yanzu? Shin wani abu ne da Ukraine ta yi la'akari da shi ko kuma saboda ta tsinci kanta cikin rikicin siyasa da yakin da kuma take yi da Rasha ne? Jami'an diflomasiyyar Ukraine kamar Subkh na tunanin cewa zurfafa dangantaka da nahiyar za ta iya haifar da karin matsin lamba kan Rasha, musamman a matakin Majalisar Dinkin Duniya.