1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Mariupol ba za mu yi saranda ba

Abdullahi Tanko Bala
March 21, 2022

Kasar Ukraine a wannan Litinin ta yi watsi da wa'adin da Rasha ta debar mata ta yi saranda da birnin Mariupol da Rashar ta yiwa kawanya.

Ukraine Mariupol | Maxar Satellitenaufnahme | Drama Theater
Hoto: Maxar Technologies/AP/picture alliance

Mukaddashin firaministan kasar ya shaidawa 'yan jarida na cikin gida a Ukraine cewa a maimakon haka yana bukatar Moscow ta kyale dubban jama'a mazauna birnin da kuma ke cikin firgici su wuce don samun taimakon jinkai. 

Tun da farko ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta baiwa UKraine wa'adi zuwa karfe biyar na safiyar Litinin 21 ga watan Maris ta bada amsa ga bukatun da Rasha ta gabatar mata.

Shugaban cibiyar tsaro ta Rasha Mikhail Mizintsev yace suna kira ga dukkan sojojin UKraine da sauran rundunoni da sojojin haya na kasashen waje su ajiye makamansu idan ba haka ba  za a dauki mataki mai tsanani akan dukkan wadanda suka ki yin saranda.

Kudancin birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa yana da muhimmanci ga yakin Vladimir Putin a Ukraine saboda mahada ce da za ta danganta sojojin Rasha a Crimea da kudu maso yamma da kuma yankunan da Rasha kuma yankunan da Rasha ta ke iko da su a arewaci da kudancin kasar.