1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na da damar kare kai a karar Rasha

Abdullahi Tanko Bala
March 15, 2023

Kotun kolin Burtaniya ta ce Ukraine na da damar kare kan ta a karar da Rasha ta shigar kan takardun lamuni. Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya baiyana hukuncin a matsayin babbar nasara

Großbritannien | Brexit - "Supreme Court" | Archivbild 2019
Hoto: Matt Dunham/AP/dpa/picture alliance

Kotun kolin Burtaniya ta ce Ukraine na da damar kare kan ta kan karar da Rasha ta shigar na lamuni wanda Ukraine din ta yi da'awar cewa Rashar tursasa mata amincewa da bashin dala biliyan uku a 2013.

Hukuncin wanda aka dade ana jira, an shigar da kara ce a 2016 tun kafin mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a 2022, wannan dai ya share fagen shari'a gadan-gadan kan batun. Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya jinjina wa hukuncin da cewa nasara ce babba

Shari'ar dai ta danganci biliyoyin daloli ne da Ukraine ta karba rance daga Rasha a karkashin tsohon shugaban kasar Viktor Yanukovich wanda ke dasawa da Rasha watanni kafin hambarar da shi a wani gagarumin bore a qwatan Fabrairun 2014, kuma jim kadan kafin Rasha ta kwace yankin Crimea na Ukraine ta shigar da shi cikin kasarta.

Ukraine ta ce tilasta mata aka yi ta karbi bashin domin hana ta sanya hannu kan yarjejeniya da kungiyar tarayyar Turai da kuma barazana ga iyakokin kasarta.

Sai dai lauyoyi da ke wakiltar Rasha sun shaidawa kotun a 2019 cewa rikicin iyaka tsakanin Ukraine da Rasha a lokacin da suka kulla yarjejeniyar ba shi da nasaba da cewa an tilasta mata ta karbi bashin. A yanzu za a ci gaba da sauraron karar a bainar jama'a