1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na fargabar hare-haren Rasha a lokacin Kirsimeti

December 23, 2025

Ukraine na fargabar ganin karuwar hare-haren Rasha yayin da mabiya addinin Kirista ke haramin bukukuwan karshen shekara. Kasar ta ce karancin kayan kare kanta barazana ne a wannan lokaci.

Shugaba Zelensky na kasar Ukraine
Shugaba Zelensky na kasar UkraineHoto: John Thys/AFP/Getty Images

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bayyana fargabar cewa Rasha na iya kai hare-hare a lokacin bukukuwan Kirsimeti, yana zargin Moscow da maimaita irin wannan hali tun farkon yaki.

Zelensky ya yi wannan gargadi ne yayin ganawa da jakadun kasashe a birnin Kyiv, inda ya ce damuwar na karuwa saboda karancin na'urorin kariya daga hare-haren sama a Ukraine.

Gargadin ya zo ne a daidai lokacin da Amurka da kawayenta a Turai ke kara kokarin diflomasiyya domin nemo yarjejeniyar da za ta kawo karshen rikicin.

Tun bayan barkewar yakin, Ukraine ta sauya kalandar bukukuwanta, inda ta fara bikin Kirsimeti a ranar 25 ga Disamba, kamar sauran kasashen Yamma.

Sai dai har yanzu, da dama daga cikin ‘yan kasar na ci gaba da bin al'adar Kiristocin Orthodox, inda ake bikin Kirsimeti a ranar 7 ga Janairu, kamar yadda ake yi a Rasha.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW