Ukraine na martanin duniya a kan kisan fararen hula
April 9, 2022Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy, ya ce yana son martani mai zafi daga kasashen duniya a kan ta'asar da dakarun Rasha suka yi a tashar jirgin kasa da ke Kramatorsk na gabashin kasar.
Shugaba Zelenskyy ya soki lamarin da kakkausar murya a daren da ya gabata, a harin da mutane 52 suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da Shugaba Biden, ya bi sahun kasashen duniya wajen yin Allah wadai da harin.
Wadanda harin ya rutsa da su a tashar ya kai dubu hudu, galibinsu mata da kananan yara da tsofaffi, wadanda ke kan shirin tsere wa dakarun Rasha.
Wasu hotuna da aka dauka a tashar jirgin kasan, sun nuno gawargwaki nannade cikin wasu jakunkunan daukar gawa da ma wani tarkacen makamai mai linzami da ke yashe a gefe.
Jami'an kasashen yamma na cewa Rashar ta sake tsarin shugabacin sojinta a Ukraine inda ta sanya wani Janar da ya jagoranci sojojinta a Syria, a matsayin jagoran yakin na Ukraine.