Ukraine na neman Rasha ta gaggauta tsagaita bude wuta
May 4, 2025
Shugaban Ukraine, Volodmyr Zelensky ya ce akwai yiwuwar a iya cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yakin da kasarsa ta kwashe fiye da shekaru uku tana yi da Rasha, inda ya nemi kawayen Kyiv da su kara matsa lamba ga gwamnatin Moscow. A lokacin da yake jawabi a wajen taron manema labarai a birnin Prague Shugaba Zelensky ya ce, Shugaba Putin ba zai dauki matakin kawo karshen wannan yakin ba, face an kara matsa mishi lamba.
Karin bayani: Ukraine ta zargi Rasha da saba alkawarin tsagaita wuta
A makon ya gabata, Shugaban Rasha ya ayyana tsagaita bude wuta na kwanaki uku, domin murnar cika shekaru 80 da nasarar da Tarayyar Soviet ta samu a kan sojojin Nazi na Jamus a lokacin yakin duniya na biyu a ranar 9 ga watan Mayun shekarar 2025. Sai dai Shugaba Zelensky ya bayyana alkawarin da mara amfani, inda ya yi kira da a tsagaita bude wutar na a kalla tsawon kwanaki 30 kamar yadda Amurka ta bukata.
Har wayau, Shugaba Zelensky ya bukaci a kara kakabawa Rasha takunkumai da kuma tallafin sojin da ake bai wa Ukraine da ma karfafa hadin kan tsaron Turai. A cewarsa hakan zai nunawa Rasha cewa, Turai za ta kare kanta.