1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na zargin Rasha da kashe wasu jami'anta

September 10, 2023

Ukraine na zargin dakarun Rasha da kashe jami'an agajinta biyu. Ma'aikar tsaron Ukraine ta ce, dakarun sun kashe Emma Ingual, dan asalin Spain da Anthony Ihnat dan Canada.

Hoto: Libkos/AP/picture alliance

Dukanninsu biyun na aiki ne da wata kungiyar agaji a kusa da birnin Bakhmut. Gwamnatin Kyiv ta bayyana kaduwarta a kan mutuwar ma'aikatan, ta na mai cewa sun sadaukar da rayuwarsu wajen kai dauki ga fararen hular da suka jikkata a yakin kasar da kuma rarraba kayayyakin agaji.

Karin bayani: Sojojin haya Wagner na ficewa daga yankin Bakhmut na Ukraine

Yankin na Bakhmut da dakarun Rasha suka karbe ikonsa tun a watan Mayun wannan shekarar, ya kasance guda daga cikin yankunan da ake gwabza kazamin fada tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a Ukraine.