1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceTurai

Ukraine: Rasha ta cika kwanaki 1000 da mamaya

Abdourahamane Hassane
November 19, 2024

An cika kwanaki 1000 da yakin Ukraine wanda kawo yanzu miliyoyin gidaje suka ruguje a sanadin hare-haren bama-bamai. Hare-haren Rasha kan Ukraine na yin tasiri a siyasar duniya da kuma irin abubuwan da suka biyo baya.

Ukraine-Krieg
Hoto: AP/picture alliance

Kwanaki 1000 da suka gabata Rasha ta fara kaddamar da hare-hare a kan Ukraine musamman ma kan iyakar arewa. A kudancin kasar, Ukraine ta kori sojojin Rasha a yankin  kogin Dnipro, kogi mafi girma a kasar.

Karin Bayani:Duniya na tir da mamayar Rasha a Ukraine

Duk da haka, manyan sassan gabashin Ukraine musamman a yankunan Luhansk, Donetsk, Zaporizhzhia da Kherson sun kasance ƙarƙashin ikon Rasha. Tun can da farko Moscow ta riga ta mamaye yankin Crimea a cikin watan Maris na shekara ta 2014. A shekaru biyu dai na yaki babu wani abinda ya canza a fagen daga da ma rayuwar al'umma. Anna Tsmykailo, da ke zaune a Kherson ta ce ta rasa komai

"Na kasance ba ni da komai, daga ni sai tuta, sai adakata,sojojin Rasha sun kwace mini gida duk abinda ke cikin gidan sun kwashe ya zama nasu; Amma dai har yanzu muna da kwarin gwiwa cewa zamu yi nasara"

Karin Bayani: Kungiyar G7 ta lashi takobin karya lagon Rasha kan yakin Ukraine

Yankin Odessa na Ukraine da aka yi wa luguden wutaHoto: Nina Liashonok/REUTERS

Sama da mutane miliyan goma ne suka rasa matsugunansu, yakin da ake yi a Ukraine ya haifar da daya daga cikin rikicin yan gudun hijira mafi girma a duniya,

 A cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR. Ya zuwa yanzu 'yan gudun hijirar Ukraine miliyan 6.7 sun sami mafaka a wasu kasashen Turai. ‘Yan makaranta ba za sa zuwa boko sai dai su dauki darasi ta hanyoyin sadarwa na intanet, bankuna da kasuwanni da asibitocin a wasu wuraran suna aiki a wasu wurin kuma a rufe suke

Lamarin ya tsananta sosai a cewar Majalisar Dinkin Duniya, kusan kashi 40 na al'ummar kasar sun dogara ne kan taimakon jin kai. Domin biyan bukatun wadannan mutane, UNOCHA da UNHCR na bukatar agajin da ya kai dalar Amurka biliyan 4.2 Evhenia Felipenko ita ce jakadar Ukraine a Majalisar Dinkin Duniya.

Karin Bayani:Rasha ta yi ikirarin kwace wani kauye na gabashin Ukraine

Jirgi mara matuki na RashaHoto: Alexander Reka/ITAR-TASS/IMAGO

"Hare-haren da Rasha ta kai na baya-bayan nan, masu girman gaske, hade da hare-haren makamai masu linzami iri-iri kan biranen na da manufa daya tilo, ita ce tsoratar da al'ummar Ukraine, da karya son rai, da jefa Ukraine cikin duhu da sanyi. Sun kuma nuna cewa Putin baya son zaman lafiya. Yaki yake so. Yana son yaki da Ukraine. Yana son yaki da sauran duniya".

Kungiyar Tarayyar Turaida sauran kawayenta na yamma sun kakaba wa Rasha takunkumin karya  tattalin arziki duk da haka Rasha ta murmure cikin sauri saboda canjin kuɗin kuɗin ƙasar, na ruble da ya yi daraja da kuma goyon bayan da ta ke samu daga China.

Karin Bayani: EU ta bai wa Ukraine Euro miliyan 50

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock yayin ziyara a UkraineHoto: Jörg Blank/dpa/picture alliance

EU da NATO suna goyon bayan Ukraine ba kawai ta hanyar takunkumi ga Rasha ba. Ukraine na samun taimakon kudi. Misali Amurka ta bayar da gudunmawa mafi girma. Bisa kididdigar da Cibiyar Kiel mai kula da tattalin arzikin duniya ta yi, tsakanin farkon yakin a ranar 24 ga Fabrairu shekara ta 2022 zuwa karshen watan Agustan 2024,

Amurka ta ba da agajin da ya kai kusan Euro biliyan 85. Taimakon da ita kanta EU da ƙasashe mambobinta suka samar ya kai sama da Yuro biliyan 100 a lokacin. Ƙasar Burtaniya da Kanada suma suna bai wa kasar taimakon kudi

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani