1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Yakin Ukraine ya ci sojan Rasha da dama

Abdoulaye Mamane Amadou
March 25, 2022

Gwamnatin Rasha ta ce sojojinta dubu daya da 351 sun mutu a fagen daga, tun bayan da ta kaddamar da yaki da makwabciyarta Ukraine a tsakiyar watan Fabrairun da ya gabata.

Yakin Rasha da Ukraine
Hoto: Maximilian Clarke/ZUMA PRESS/picture alliance

Mataimakin babban hafsan hafsoshin sojojin Rashan Sergueï Roudskoï ne ya tabbatar da hakan, a yayin da yake ganawa da manema labarai. Roudskoï ya ce ko baya ga wadanda suka mutu, akwai wasu fiye dubu uku da 800 da suka jikkata a Ukraine tun bayan da suka soma gwabza yaki da kasar. 

Rasha ta yi kakkausar suka ga matakin kungiyar tsaro ta NATO na taimakawa Ukraine da makaman kare kanta, tana mai cewa hakan ka iya kara dagula al'amurra da haddasa yawan wadanda fadan zai yi wa illa.