Ukraine ta amince da hulɗar kasuwanci da EU
September 16, 2014Majalisar dokokin Ukraine ta amince da yarjejeniyar kasuwanci mara shingen nan mai sarkakiya, tare da Tarayyar Turai. Sun amince da yarjejeniyar ne, a lokaci guda da majalisar dokokin Turan da ke birnin Straßbourg yayin da suke kallon juna ta hotunan bidiyo. Wannan damar shiga kasuwanci mara shinge wanda ke ɗaya daga cikin abubuwan da ya yi mafarin rikicin Ukraine da mahukuntan Mosko, wanda kuma ka iya kara rura wutar rikicin zai fara aiki a shekara ta 2016.
Da farko dai majalisar dokokin a Kiev ta amince da dokar da ta bai wa yankin gabashin Ukraine ikon cin gashin kai, ta kuma amince da yin afuwa ga duk 'yan tawayen yankin, wanda da yin hakan, ke nuna cewa yankin ya sami ikon gudanarwa.
Haka nan kuma wasu tanade-tanaden sun ƙunshi ikon gudanar da zaɓe, da girka jami'an tsaro da ma damar gudanar da wasu aiyyukan hadin kai tare da wasu yankunan da ke iyaka da Rasha