1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine ta amince da kudirin iya fuskantar hukunci daga ICC

Mouhamadou Awal Balarabe
August 21, 2024

Majalisar dokokin Ukraine ta kada kuri'ar amincewa da yarjejeniyar Rome da ta kafa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC. Amincewar na zama daya daga cikin matakan cimma burinta na shiga cikin Tarayyar Turai EU.

Zauren majalisar dokokin Ukraine
Zauren majalisar dokokin UkraineHoto: Mykola Lazarenko/Ukrainian presidential press service/TASS

 Akasarin 'yan majalisun kasar sun yi na‘am da kudirin da Ukraine ta dauka na karfafa matakin zama memba na ICC. Dama Ukraine ta amince da wani bangare na binciken da kotun ta duniya ta gudanar kan laifukan da ake zargin aikatawa a rikicin da ya fara a shekara ta 2014 a kasar, kafin ya rikide i zuwa mamayar da Rasha ta yi  a Ukraine a 2022. Idan za a iya tunawa, kotun ICC ta bayar da sammacin kama shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da wasu jami'ai kan laifukan da ake zarginsu da aikatawa a kasar.

Karin bayaniKotun ICC ta cika shekaru 20 da kafuwa

Ukraine da kuma Rasha ba su taba zama cikakkun mamba na kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ba. Amma dai amincewa da Icc ya kasance daya daga cikin matakai da suka wajaba a kan Kyiv idan tana son cimma burinta na shiga cikin Kungiyar Tarayyar Turai.