1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta ce a shirye take ta dakatar da hare-harenta

Binta Aliyu Zurmi
October 11, 2026

Shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine ya ce a shirye suke su dakatar da kai hari kan matatun mai na Rasha idan har Kremlin ta dakatar da hare-haren da take kai wa ababen more rayuwa a Ukraine.

Ukraine Kyjiw 2026 | Ukraine-Nordic-Baltic Summit | Wolodymyr Selenskyj bei Pressekonferenz
Hoto: Antti Aimo-Koivisto/Lehtikuva/picture alliance

Wannan sanarwar ta Kyiv na zuwa ne kwana guda bayan rikici da ya barke tsakanin Trump da Zelensky biyo bayan sanarwar Trump na sayen makamashin dizel zuwa kasuwannin duniya domin samun saukin takunkuman da aka kakaba mata.

Zelensky ya bayyana yarjejeniyar da Washington da Kremlin suka cimma ta fidda makamashin dizel zuwa Amurka a matsayin mai rauni da kuma ke goyon bayan ci gaba da kai musu hari.

Rasha ta kaddamar da hare-hare kan kayayyakin samar da makamashi na Ukraine tun bayan mamayarta a kasar a shekarar 2022.

Kamfanin samar da makamashi mai zaman kansa na Ukraine ta sanar da sabbin katsewar wutar lantarki a babban birnin Kyiv .

Karin Bayani:Trump ya gargadi Zelensky kan kai wa matatun man Rasha hari