1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Ukraine ta ce ta tana dab da shiga EU

November 2, 2023

Gwamnatin kasar Ukraine ta bayyana kwarin gwiwa kan cimma burinta na shiga kungiyar Tarayyar Turai EU, batun za a tattauna a kansa kafin karewar wannan shekara.

Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytry Kuleba
Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytry KulebaHoto: Olivier Matthys/AP Photo/picture alliance

Da yake magana gabanin taron da za a Berlin babban birnin kasar Jamus, ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya ce kasarsa na kan gwadabe duk da cewa tana fama da yaki.

A cewar Minista Kuleba, Ukraine ta kammala cika dukkanin wajiban da suka wuce matakai na majalisu bayan tarin sauye-sauyen da suka yi.

Kwanaki kafin kaddamar da yaki a kanta da a ranar 24 ga watan Fabrairun bara Rasha ta yi ne dai, Ukraine din ta mika bukatar shiga Tarayyar Turai a hukumance.

Watanni bakwai bayan nan ne kuma kungiyar ta EU ta yi na'am da bukatar, kuma goyon baya mai karfi daga kungiyar ya biyo baya.