Ukraine ta cika shekaru 40 da hatsarin nukiliyar Chernobyl
April 26, 2026
Talla
Shugaban kasar Volodymyr Zelensky zai halarci taron tunawa da masana'antar.
A Kiev da sauran biranen, an shirya bukukuwa da suka hada da lokaci na yin shiru da kade-kade da nuna fina-finai gami da shimfida furanni don girmama wadanda bala'in na shekarar 1986 ya rutsa da su.
Ana kuma sa ran gudanar da bukukuwan tunawa da su a kasashen Belarus, Rasha da sauran tsoffin jamhuriyar Tarayyar Soviet.
Masana sun yi kiyasin duban mutane ne suka rasa rayukansu sanadiyar wannan hatsarin. Fiye da mutane 100,000 ne aka kwashe daga yankin mai nisan kilomita 30 da tashar da ta daina aiki a yanzu.