1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Ukraine ta doke Slovakiya da ci 2-1 a wasan rukuni

Mouhamadou Awal Balarabe
June 21, 2024

Nasarar da Ukraine ta samu a kan Slovakiya da ci 2-1 a wasan rukunin E ya sa kasashe uku: Romaniya da Ukraine da Slovakiya samun maki uku kowacce, yayin da Beljiyam ba ta da maki ko daya a wannan rukunin E.

Dan wasan Ukraine Roman Yaremchuk ya nuna jin dadi bayan da ya ci kwallo
Dan wasan Ukraine Roman Yaremchuk ya nuna jin dadi bayan da ya ci kwalloHoto: ASSOCIATED PRESS/picture alliance

Slovakiya ta yi fatan samun nasara a Düsseldorf domin hayewa mataki na gaba na gasar Euro 2024, amma hakarta ba ta cimma ruwa ba. Hasali ma,  'yan wasan kasar Ukraine ba su sakar mata mara ba saboda su ma suna sha'awar samun kyakkyawan matsayi bayan da suka dibi kashinsu a hannun Romaniya da ci 3-0 a wasan farko.

Duk ma da cewar Ukraine ta fara wasan da kafar hagu inda Ivan Schranz na Slovakioya ya zura mata kwallo tun a minti na 17 da fara wasa, amma ta farfado daga bisani, inda minti tara bayan dawowa hutun rabin lokaci Mykola Shaparenko ya farke kwallon da ake binsu. Sannan minti goma kafin a yi busan karshe, Roman Yaremchuk ya yi wa mai tsaron gidan Slovakiya tsarki, lamarin da ya sa aka tashi wasa Ukraine na da ci biyu yayin da Slovakiya ke da daya. A yanzu, kungiyoyi uku: Romaniya da Ukraine da Slovakia na da maki uku-uku, yayin da Beljiyam ba ta da maki ko daya a wannan rukunin E.

Spain ta tsira da kyar a hannun Italiya

Dan wasan Spain Nico Williams na daga cikin wadanda suka bayar da gudunmawa sosaiHoto: Alberto Estevez/Agencia EFE/IMAGO

A ranar Alhamis 20.06.2024 d maraice, La Roja ta Spain ta samu rinjaye a wasan da ya gudana a birnin Gelsenkirchen, amma ta kasa shammatar mai tsaron gida Italiya Gianluigi Donnarumma. Sai dai daga karshe, Italiya ta ba da kai bori ya hau inda dan wasanta Riccardo Calafiori ya zura kwallo a ragarsu bayan matsin lamba da suka sha.

Wannan nasara ta 1-0 ta yi matukar faranta ran koci Luis de la Fuente, wanda ke ganin kungiyarsa ta Spain za ta ci gaba da ganin haske idan ta jajirce: Ya ce: "Na ji dadin wannan sakamakon, ganin cewa mun doke wata babbar kungiya da ke rike da kofin gasar kwallon kafa ta Turai. Bugu da kari ma, na ji dadin salon da wasan ya gudana. A yayin da gasa ke ci gaba da gudana, abokan hamayyarmu na kara sanin kaifinmu kuma suna neman rikitar mana da dabaru. A lokacin da na fara horas da Spain, na bayyana cewar babu wata kungiyar da ta fi tamu. Kuma ina kan bakata har yanzu, musamman idan muka ci gaba da yin aiki a yanayi na himma da tawali’u."

 Spain ce ke kan gaba a rukunin B da maki shida yayin da Italiya ke biya mata baya a matsayi na biyu da maki uku. Su kuwa Kuroshiya da Albaniya suna da maki daya kowaccen su.

Ingila: Babu yabo kuma babu fallasa

Karfi ya zo daya tsakanin 'yan wasan Ingila da na DanmarkHoto: REUTERS

A rukunin C kuwa, Ingila ta yi kunnen doki da Denmark 1-1 a karawa da ta yi a birnin Frankfurt. Da farko dai, masharhanta wasanni sun bayyana kungiyar Three Lions ta Ingila a matsayin daya daga cikin wadanda ake kyautata wa zaton ganin badi. Mai yiwuwa shi ya sa magoya bayansu suka yi ta yi wa 'yan wasa Ingila ihu don nuna rashin jin dadinsu, lamarin da mai tsaron gida Jordan Pickford ya bayyana cewar har yanzu da sauran fata. Ya ce: "Babu wani wasa mai sauki. kowa zai so mu samu nasara, amma ba abu ne mai sauki ba. Mun samu maki daya, kuma a yanzu muna da maki hudu bayan wasanni biyu. Mu ne ke kan gaba kuma a yanzu muna mai da hankali kan wasan da za mu ranar Talata."

Ingila ce ke kan gaba a rukunin C da maki hudu, ma'ana ta zarta Denmark da kuma Sloveniya da maki biyu wacce ta yi kunnen doki da Sabiya 1-1.