1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta harba makamai kirar Birtaniya cikin Rasha

November 21, 2024

Ukraine ta harba makamai masu linzami da ke cin dogon zango da Birtaniya ta kera zuwa wasu yankunan Rasha, duk kuwa da gargadin da gwamnatin Moscow ke ci gaba da mata.

Ukraine ta harba makamai masu linzami kirar Birtaniya cikin Rasha
Ukraine ta harba makamai masu linzami kirar Birtaniya cikin RashaHoto: Malcolm Park/Avalon/picture alliance

Tun a shekarar 2023 ne Birtaniya ta fara bai wa UKraine makaman masu linzami da ke cin dogon zango samfarin Storm Shadow, sai dai bisa sharadin yin amfani da su a cikin yankunan da ke karkashin ikon Ukraine din. Ana dai ganin bisa dukannin alamu, Birtaniya ta bi sahun gwmnatin Shugaba Joe Biden na Amirka, na dage takunkumin amfani da makamanta masu linzami a cikin Rasha.

Karin bayani: Yakin Rasha da Ukraine ya dauki sabon salo

Sai dai kuma kakakin Firanminstan Birtaniya, ya ce offishinsa bai zai ce uffan ba dangane da harin da Ukraine din ta kai. Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya yi gargadin cewa, amfani da makaman Amirka da Birtaniya wajen kai mishi hari tamkar kungiyar tsaro ta NATO ta shiga rikici kai tsaye ne da Rasha.