1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta kaddamar da hare-hare a Rasha

March 21, 2026

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce, Ukraine ta kai hare-haren jirage matuka kimanin 280 cikin dare a sassa daban-daban na Rasha.

Hoto: Stringer/REUTERS

Gwamnan yankin Rostove ya ce an kakkabo jiragen 90 a kudancin yankin daga cikin wadanda Ukraine ta harba Rasha cikin dare. Yayin da kuma magajin garin Moscow, Sergei Sobyanin ya ce an kakkabo wasu 27 da aka harba su zuwa a babban birnin kasar. Sai dai kuma gwamnan yankin Saratov ya ce, mutane biyu sun jikkata a harin jiragen da ya lalata gidaje da dama a kudu maso yammacin yankin.

Karin bayani: Ukraine ta kai wa Rasha kazamin hari a masana'antar kera makamai

Ana dai sa ran masu tattaunawa na Ukraine da Amurka kan kawo karshen yakin  su gana a wannan Asabar din, a cewar Shugaba Volodmyr Zelenskyy na Ukraine. A cewarsa, Kyiv za ta nema karin haske daga jami'an Amurka a zaman tattauna na kwanaki uku da Rasha, da aka dage a watan da ya gabata sakamakon rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.