SiyasaTurai
Ukraine ta kai hari kan jiragen saman Rasha
August 30, 2023Talla
Harin wanda aka kai filin jirgin sama na Pskov mai tazarar kilomita 700 daga kan iyakar Ukraine ya kasance na baya bayan nan da aka kai cikin Rasha tun bayan da Kiev ta yi alkawarin mayar da martani har cikin Rasha.
Sai dai gwamnan lardin Mikhail Vedernikov ya fada a shafukan sada zumunta cewa sun dakile harin na filin jirgin saman Pskov kuma babu wanda ya rasa ransa, sannan suna nazarin ta'adin.