1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine ta kai sabbin hare-hare kan Rasha

August 15, 2026

A baya-bayan nan Kyiv ta kara yawan farmaki da ta ke kai wa kan muhimman wurare a Rasha.

A baya-bayan nan Kyiv ta kara yawan farmaki da ta ke kai wa kan muhimman wurare a Rasha
A baya-bayan nan Kyiv ta kara yawan farmaki da ta ke kai wa kan muhimman wurare a RashaHoto: Vantor/Handout/REUTERS

Ukraine ta ce hare-haren da ta kai da makamai masu linzami masu cin dogon zango sun lalata wani filin jirgin saman sojin Rasha da kuma cibiyar makamai masu linzami a Rasha.

Kyiv ta ce wuraren na taimaka wa Rasha wajen kai hare-hare sannan suna daga cikin inda kasar ke gina cibiyoyin intanet irin na Starlink.

Harin Ukraine ya kashe mutum 13 a Rasha

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce an yi amfani da makamai masu linzami kirar Flamingo wajen kai hari kan cibiyar, wadda ke da nisan kusan kilomita 900 daga iyakar Ukraine.

Ya ce manufar harin ita ce matsa wa Moscow lamba ta kawo karshen yakin da aka shafe fiye da shekara hudu ana gwabzawa.

Ukraine da NATO sun tattauna kan karin makaman kariyar sararin samaniya

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Zelensky ya ce, "rage karfin Rasha na ci gaba da yaki muhimmin abu ne.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW