1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta musanta karbe iko da birnin Soledar

January 12, 2023

Bayan sanarwar kwace iko da birnin Soledar a Ukraine, gwamnatin kasar ta karyata ikirarin da Rasha ta yi a kan wannan batu. A gefe guda kuwa Rasha ta sauya kwamandanta na yaki.

Hoto: Clodagh Kilcoyne/REUTERS

Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine, ya ce har yanzu ana ci gaba da gwabza fada a yankin birnin Soledar da ke a gabashin kasar, yankin kuma da sojojin hayar Rasha na kamfanin Wagner ke cewa su ke rike da shi a yanzu.

Cikin sakon da ya gabatar a daren da ya gabata, Shugaba Zelensky wanda ya ce an lalata birnin ya kuma ce Rasha da 'yan farfagandarta na kokarin nuna cewa sun yi nasara a Soledar, alhalin kuwa ana can ana bata kashi.

A ranar Laraba ne dai shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin ya yi ikrarin cewa sun karbe garin na Soledar.

Wannan dai na zuwa ne yayin da Rasha ta sanar da nadin Janar Valery Gerasimov a matsayin sabon kwamandan rundunonin hadin gwiwa da ke yaki a Ukraine.

Shi dai Janar Valery Gerasimov, ya maye gurbin Janar Sergey Surovikin ne wanda aka bai wa mukamin cikin watan Oktobar bara.