1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na son a kara yawan makamashi

Ramatu Garba Baba
March 26, 2022

Shugaba Zelensky ya nemi taimakon kasar Katar wajen bunkasa yawan man da take fitarwa a kasuwannin duniya don karya lagon Rasha da ke mata barazana da makami mai guba.

Ukraine-Krieg - Katar - Videobotschaft von Präsident Selenskyj Doha
Hoto: Mohammed Dabbous/AA/picture alliance

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky yayi kira ne ga kasar Katar, kan ta kara yawan makamashin da take fitarwa, ya ce yin hakan kadai ne zai taimaka mata kalubalantar matakin Shugaba Vladimir Putin na Rasha, yara fiye da dari daya sun mutu tun bayan soma yakin a watan Febrairun da ya gabata, yanzu akwai yiyuwar Rasha tayi amfani da makami mai guba a mamayar da kasarsa ke yi wa Ukraine. 

Shugaban ya isar da sakon nasa a gaban manyan mukaraban gwamnatin na Katar da suka halarci taron ta bidiyo a birnin Doha, cikin mahalartar taron na wannan Asabar har da sarkin Katar Tamim bin Hamad al-Thani. Manyan kasashen duniya na ci gaba da kokarin ganin sun taimaka ma Ukraine a daidai lokacin da yakin ke ci gaba da lakume rayuka da kuma tilasta wa miliyoyi zama 'yan gudun hijira.