Ukraine: Zelenskyy ya roki Isra'ila ta ba shi makamai
March 20, 2022Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya nemi tallafin makamai daga Isra'ila, yana mai tunasar da Isra'ila yawan Yahudawan da ke zaune a Ukraine.
Shi kan shi Shugaba Zelenskyy dai Bayahude ne, kuma ya nuna bacin ransa ga 'yan majalisar Isra'ila kan yadda Rasha ta kai hari a kushewar tunawa da kisan kiyashin Yahudawan nan na Holocaust da ke a Ukraine.
Kafin yanzu dai shugaban na Ukraine ya yi irin wannan jawabin ga 'yan majalsiar dokokin Amirka da Jamus da Kanada, inda yake ci gaba da neman a taimaka masa, a zo a yaki dakarun Rasha.
Wannan na zuwa ne a yayin da mahukunta a birnin Kiev suka ce dakarun Ukraine sun yi nasarar halaka manyan kwamandojin yakin Rasha a wannan Lahadi. Sai dai kuma sun zargi Rasha da kokarin kai wa biranen da rikicin bai shafe su ba hari.