1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta soke taron ƙolin EU na Yalta

May 8, 2012

Ma'aikatar harkokin wajen Ukraine da ke birninn Kiev ta ce ta soke taron ƙolin na EU ne saboda shugabannin ƙasashen Turai kimanin 10 sun ƙaurace masa.

EU heads of state pose for a group photo during an EU summit in Brussels, Thursday March 1, 2012. From left to right, first row: EU foreign policy chief Catherine Ashton, Dutch Prime Minister Mark Rutte, Latvian Prime Minister Valdis Dombrovskis, Greek Prime Minister Lucas Papademos, European Commission President Jose Manuel Barroso, French President Nicolas Sarkozy, Lithuania's President Dalia Grybauskaite, Denmark's Prime Minister Helle Thorning-Schmidt, European Council President Herman Van Rompuy, Cypriot President Dimitris Christofias, Romania's President Traian Basescu, European Parliament President Martin Schulz, Irish Prime Minister Enda Kenny, Italy's Prime Minister Mario Monti, Luxembourg's Prime Minister Jean-Claude Juncker, Slovakia's Prime Minister Iveta Radicova, General Secretariat of the EU Council Uwe Corsepius. Second row, from left to right: Croatia's Prime Minister Zoran Milanovic, Poland's Prime Minister Donald Tusk, Hungarian Prime Minister Viktor Orban, Belgium's Prime Minister Elio Di Rupo, Spain's Prime Minister Mariano Rajoy, Swedish Prime Minister Fredrik Reinfeldt, Czech Republic's Prime Minister Petr Necas, Slovenia's Prime Minister Borut Pahor, Portugal's Prime Minister Pedro Passos Coelho, German Chancellor Angela Merkel, Finland's Prime Minister Mari Kiviniemi, Austrian Chancellor Werner Faymann, Bulgarian Prime Minister Boyko Borissov, Estonia's Prime Minister Andrus Ansip, British Prime Minister David Cameron, Malta's Prime Minister Lawrence Gonzi. (Foto:Geert Vanden Wijngaert/AP/dapd)
Hoto: dapd

Ƙasar Ukraine ta soke taron ƙoli da aka shirya gudanarwa a birnin Yalta sakamakon sanar da aniyarsu na ƙin halartansa da wasu shugabanni na ƙasashen Turai suka yi. Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar da ke birnin Kiev da ta bayar da wannan sanarwa ba ta ƙayyade ranar da taron na koli zai gudana nan gaba ba.

Shugabannin ƙasashen Turai sama da goma ciki kuwa har da shugaba Joachim Gauk na Jamus ne suka ƙaurace ma taron na Ukraine, sakamakon cin zarafin tsofuwar firaministan ƙasar wato Julia Timochenko da gandurorbobi ssuka yi a gidan yari. Wasu daga cikin shugabannin na Turai ciki har da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel suka ce ba za su halarci bikin buɗe wasannin kwallon kafa na ƙasashen Turai da Ukraine za ta ɗauki baƙwanci ba, matiƙar ba a sako Timochenko ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar