1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine ta yaba da hada sabon babban jami'in NATO

Suleiman Babayo AH
June 26, 2024

Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine ya jinjina kan nadin Firaminista Mark Rutte na kasar Netherlands a matsayin sabon Babban Sakataren kungiyar tsaron NATO-OTAN inda zai karbi ragama a watan Oktoba.

A wannan Laraba Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine ya nuna jinjina game da amincewa da hada Firaminista Mark Rutte na kasar Netherlands mai barin gado a matsayin sabon Babban Sakataren kungiyar tsaro ta NATO-OTAN. A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa sada zumunta na Intanet, shugaban na Ukraine ya ce yana sane da cewa sabon sakataren na kungiyar tsaron NATO, Rutte mutum ne mai tsayuwa kan manufa.

Tuni dai kasar Rasha wadda ta kaddamar da hare-haren mamaya kan Ukraine, take cewa babu abin da zai sauya game da sabon nadin, domin Rasha ta dauki kungiyar tsaron NATO a matsayin abokiyar-gaba.

Ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa ake sa ran Mark Rutte firaministan Netherlands mai barin gado zai fara aiki a matsayin sabon Babban Sakataren kungiyar tsaron NATO-OTAN.