1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiev ta zargi Moscow da kai harin guba

Abdul-raheem Hassan
July 2, 2022

Kasar Ukraine ta zargi sojojin Moscow da harba bama-bamai na guba a tsibirin Zimiinyi ko 'Snake Island' jim kadan bayan da dakarun Rasha suka janye daga mahimman wurare a Tekun Bahar Maliya.

Ukraine | Schlangeninsel (Zmiinyi Island, Snake Island)
Hoto: 2022 Maxar Technologies via AP/picture alliance

Wani babban kwamandan sojojin Ukraine, ya ce wasu jiragen yakin Moscow da suka taso daga yankin Creamea da ke karkashin ikon Rasha, sun yi ta zazzago sinadaran guba na "phosphorus" a tsibirin, ya kuma wallafa bidiyon lamarin a shafin Telegram a mastayin hujja.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da sojojin Rasha suka fice daga tsibirin a wani abin da Moscow ta bayyana a matsayin "karimcin fatan alheri."