Ukraine taki aminta da shigar motocin Rasha
August 12, 2014Hukumomin kasar Ukraine, sun ce bazasu yarda jerin motocin kayan agaji na kasar Rasha su shiga kasar ta Ukraine ba, inda suka ce sai dai tun daga bakin iyaka a sauke kayan, sannan a sake loda su cikin wasu motoci na kungiyoyin agaji dake cikin kasar ta Ukraine. Wadannan kalammai sun fito ne daga bakin Valeri Tchaly mataimakain shugaban fadar shugaban kasar ta Ukraine a wani jawabi da yayi a gaban manema labarai, inda ya kara da cewa, ba su yarda ba ace ma'aikatan ofishin ministan agaji na kasar Rasha suyi rakiyar kayan agajin da Rasha ta bayar ba.
Rasha dai ta aike a kalla motoci 280 dauke da kayayakin agaji na abinci da dai sauran magungunna, ga al'ummar gabacin kasar ta Ukraine da yaki ya rutsa da da su, inda hukumomin na Ukraine suka ce basu san abubuwan dake cikin motocin na Rasha ba.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu