1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miliyoyin mutane na hijira a cikin Ukraine

March 18, 2022

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan shida da rabi sun bar muhallansu a cikin Ukraine, yayin da wasu fiye da miliyan uku suka fice daga kasar zuwa wasu kasashe makwabta bayan da Rasha ta kaddamar da yaki.

Wasu 'yan gudun hijirar Ukraine
Hoto: MDR

Bayan wani harin bam da sojojin Rasha suka kaddamar a wani gidan wasan kwaikwayo a Ukraine, hukumomi sun ce daruruwan mutane sun makale a cikin baraguzan ginin. Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amirka ta gargadi China ta tsawata wa babbar kawarta Kremlin da ke aikata lafukan yaki a Ukraine.

Da yake magana da Shugaban Rasha Vladmir Putin ta wayar tarho, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana matukar damuwa game da makomar Mariupol na Ukraine ya kuma bukaci stagaita wuta don kai agaji a birnin.