1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus za ta kara wa Ukraine tallafi

September 18, 2023

Gwamnatin Jamus ta sanar da shirin kara wa Ukraine tallafi mai kabri da kudade na makamai domin fuskantar dakarun mamaya na Rasha da ke matsa lamba a wasu sassan kasar.

Ukraine za ta samu karin tallafi daga Jamus
Ukraine za ta samu karin tallafi daga JamusHoto: Nikita Jolkver/DW

Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius ne ya sanar da hakan a wannan Litinin (18.09.2023 inda ya ce za a bai wa Kiev wani sabon kunshin taimako da ya ta tashi a miliyan 400 na yuro domin kara mata karfin soja.

Karin bayani: Jamus za ta saya wa Ukraine makamai

To sai dai yayin da yake sanar da wannan sabon kunshi na taimakon, ministan ba yi ba karin bayani kan batun aike wa Ukraine da makamai masu linzami masu cin dogon zango samfarin ''Taurus'' kamar yadda mahukutan Kiev suka bukata.

Karin bayani: Jamus za ta tallafa wa Ukraine da tankokin yaki

Wanda tallafi zai karawa dakarun Kiev kwarin guwiwa kan farmakin suka kaddamar a karshen watan Juni domin fatattakar dakarun mamaya na Rasha da suka karbe iko da yankuna da dama na kasar.