1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine za ta shiga kungiyar tsaro ta NATO

October 1, 2022

Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine ya ce kasarsa za ta mika takardar gaggawa ta neman shiga kawance cikin kungiyar nan ta tsaro wato NATO.

Ukraine | Wolodymyr Selenskyj
Hoto: Ukrainian Presidential Press Office/Planet Pix/ZUMA Press Wire/picture alliance

Shugaban na Ukraine ya ce hakan wani mataki na tabbas ne da kasar ta dauka domin nuna himmatuwarta ga bukatar shiga kungiyar.

Mr. Zelenskyy ya ce ba zai taba yin wata tattaunawar sulhu da Rasha ba, muddin dai Vladimir Putin ne ke shugabantar kasar.

Ya yi alkawarin cewa shugaban kawai a Rasha da zai yi zaman sulhu da shi, sai wani sabon ba kuma na yanzu ba.

Kafin wannan sanarwa ta shugaba Zelenskyy dai, sai da wasu jiga-jigan majalisar tsaron kasar suka yi wata ganawa a game da abin da Rasha ta yi na ayyana shigar da wasu yankunan Ukraine a cikinta a ranar Juma'a.