1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaba Zelenskyy ya kai ziyara Britaniya

Ramatu Garba Baba
February 8, 2023

Shugaba Volodymr Zelenskyy ya nemi taimakon Britaniya don ganin kasarsa ta yi nasara a kan Rasha da ke tsananta hare-hare a gabashin kasar ta Ukraine.

Firaminista Sunak da Shugaba Zelenskyy
Firaminista Sunak da Shugaba ZelenskyyHoto: Victoria Jones/PA via AP/picture alliance

A wannan Laraba, shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya bar kasar da ke tsakiyar yaki da Rasha don ziyartar Britaniya, tuni ya sa isa birnin Landan in da ya gana da firaminista Rishi Sunak da ya masa tarba ta musanman.

Ziyarar ta ba-za-ta na zuwa ne a daidai lokacin da Zelenskyy ke kara neman taimakon makaman yaki daga manyan kasashen duniya da zummar kare kasarsa daga mamayar Rasha, da ya ce, hare-haren da ta kai wa Ukraine a wannan makon sun kasance mafi muni tun bayan soma fadan a watan Febrairun bara.

Har wa yau a gobe Alhamis, Shugaba Zelenskyy zai halarci taron shugabanin kasashen tarayyara Turai a birnin Brussels na kasar Beljiyam, karon farko da zai yi jawabi a gaban taron amma ba ta bidiyo ba kamar yadda ya saba tun bayan soma yaki da Rasha.